Daga Sani Dan Bala Gwarzo
Shugaban karamar hukumar Fagge a jihar Kano Hon Salisu Usman Masu ya tabbatar da aniyarsa na cigaba da tallafawa matasa da ayyukanyi a Fagge da kewayenta.
Hon Salisu Masu ya ce duba da yadda matasa a wannan lokaci ke fama da rashin ayyukanyi yasa majalisar karamar hukumar Fagge tashi tsaye domin inganta rayuwar matasan.
Yace nan da Wani lokacin sai an nemi marasa aikinyi a Fagge an rasa.
Shugaban a wata hira da wakilinmu Sani Dan Bala Gwarzo,yace a kasa da watanni biyu ya samawa matasa 300 aikinyi.
Yace hakan zai taimaka matasan su dogara da kansu.
Ya kuma nuna gamsuwarsa kan yadda matasa da dama a Fagge suka daina shiga ayyukan fadan daba kwacen waya ,saboda aikin da ya samarwa matasa.
Hon Masu ya kara dacewa daga zuwnasa a matsayin Shugaban karamar hukuma ,Fagge ta kubuta daga masu kwacen waya ko fadan daba.
Shugaban hukumar ta faggen ya kuma ce fannin ilimi a karamar hukumar ya samu cigaba tun bayan zuwansa a matsayin jagoran yankin.