Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da sabon tsari da zai bayar da tukuici ga baƙin haure da suka shigo ƙasar ta haramtacciyar hanya idan har suka amince su fice daga ƙasar da kansu su koma kasashensu.
Wannan sabon tsarin, wanda ma’aikatar tsaron cikin gida ta kasar ta sanar, na da nufin rage cunkoson da ke barazana ga hukumomin kula da shige da fice a Amurika.
Trump tace waɗanda suka amince su fice daga kasar domin kashin kansu, za a basu Dala 1,000, kuma, ba za su kasance cikin jerin mutanen da za a kama ko tilasta musu ficewa ba.
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace.
A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa ƙasar Honduras.
Tun bayan da Trump ya sake komawa kan kujerar mulki a watan Janairu, ya gindaya sabbin matakai masu tsauri don hana baƙin haure shiga ƙasar.
Wasu daga cikin waɗannan matakan na haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake amfani da tsofaffin dokokin wanda suke da alaka da zamanin yaƙi wajen aiwatar da su.

