Kungiyar yan Fansho ta Najeriya (NUP) ta bayyana cewa duk wani ɗan fansho da bai zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben shekarar 2027 ba, ya ci amanar ƙungiyar da kuma alƙawarin da suka ɗauka na goyon bayan ci gaban jihar.
Mataimakin Shugaban ƙungiyar reshen Arewa maso yammacin Najeriya Comrade Salisu Ahamad Gwale, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron da kungiyar yan fansho ta jihar Kano ta shirya a Kano domin karrama Ahamad Gwale da kuma gabatar da sabbin shugabanin Kungiyar.
Gwale ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nuna ƙauna da kulawa ta musamman ga ‘yan fansho ta hanyar biyan bashin fansho da alawus,da tallafi, da kuma sake farfaɗo da martabar tsoffin ma’aikata a jihar.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo mana da mutuncinmu. Ya biya mu bashi, ya saurari korafe-korafenmu. Duk wani ɗan fansho da bai zaɓe shi a 2027 ba, lallai ya ci amanarmu,” in ji shi.
Tsohon Shugaban Kungiyar ta fansho reshen Kano mai jiran gado ya nemi sabbin shugabanin Kungiyar a Kano da mukaddashin Shugaban Kungiyar a Kano Kwamared Shu’aibu Musa Jibiril.
Ya ƙara da cewa kungiyar za ta ci gaba da mara wa gwamnatin NNPP baya, tare da yin kira ga gwamnati da ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su inganta rayuwar ‘yan fansho a fadin jihar.
Anasa jawabin mai rikon mukamin Shugaban Kungiyar yan fansho na jihar Kano, kwamred Shu’aibu Musa Jibiril yaci alwashin cigaba da fadi tashi domin tabbatar da walwalar yan fansho a Jihar

