Hukumar Kula da ganin wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal na shakerar 2025 ba a ƙasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Lahadi 30 ga watan Maris na shekarar 2025 daidai da 30 ga watan Ramadan 1446 bayan Hijra inda a bana za’a gabatar da azumi guda 30 kenan.
Don haka ranar Litinin 1 ga watan Maris na shekarar 2025 itace ta kasance ranar Sallah karama.
Shafin sada zumunta na Haramain ya rawaito cewa kwarraru masu binciken ganin wata 20 ne suka zauna duba jaririn watan na Shawwal,amma ba’a ganshi ba.
TST Hausa ta rawaito cewa ,dama tuni masana kimiyar taurari da sararin samaniya suka shaida cewa azumin na bana 30 za’a yi maimakon 29 saboda kusufin rana da ta rufe wata da aka samu a ranar ta 29 ga watan Ramadan.
Anga yadda gajimare ya rufe yammacin kasar ta Saudiyya,Inda ya kamata ace anga watan na Shawwal

