Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Asabar 29 ga watan Maris 2025.
An ga watan ne a yankuna da dama na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata ya bayyana.
Yanzu dai Saudiyya ta kammala azumin Ramadan na bada da yakai ga yan kasar sun gudanar da azumin guda 29.
TST Hausa ta rawaito cewa gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal na shakerar 1446 itace tayi daidai da 30 ga watan Maris 2025.
An kai ruwa rana kafin tabbatar da ganin jaririn watan na Shawwal, Sakamakon yadda masana kimiyar taurari sukayi hasashen cewa ba lalle ne aga watan ba.
Shafin Sada zumunta na Haramain ya rawaito cewa a kalla kwarraru masu binciken ganin wata 20 ne suka zauna domin duba jaririn watan a masarautar Saudiyya.

