Farfesa Lateef Oladimeji Sanni, kwararre a fannin aikin gona kuma masani a kan kayan amfanin gona da ‘ya’yan itatuwa na yankunan dake da zafi, ya bayyana muhimman cin ayaba da safe, musamman ga lafiyar jiki da kwakwalwa.
Ya lissafo wasu daga cikin mahimmacin cin Ayaba ga lafiyar jama’a da safe.
1.Ƙarin Kuzari.
Ayaba na dauke da sinadarin carbohydrates da sukari na halitta kamar su glucose, fructose da sucrose – wadanda jiki ke canzawa zuwa kuzari cikin sauri.
Wannan na da matukar amfani da safe bayan jikin ya shafe dare yana yin azumi ba tare da samun abinci ba.
2.Aikin narkar da Abinci.
Ayaba na dauke da fiber mai narkewa da wanda ba ya narkewa, wanda ke taimakawa wajen narkewar abinci da kuma saukaka yin bayan gida.
Hakan yana taimakawa wajen hana kumburi da gyaran hanji gaba ɗaya.
3.Taimakawa daidaiton sukarin Jini.
Ko da yake ayaba na dauke da sukari na halitta, tana da karancin glycemic index, wanda ke nufin tana sakin sukari a jiki a hankali.
Wannan yana taimakawa wajen hana tashin hankali na sukari a jini, musamman idan an ci ayaba tare da wasu abinci a matsayin cikakken karin kumallo.
4.Samar da karin Potassium.
Ayaba na dauke da sinadarin potassium da yawa ,wato wani sinadari ne mai matukar muhimmanci da ke da rawar gani wajen daidaita matsayin jini da kuma kiyaye lafiyar zuciya.
5.Inganta yanayin lafiyar zuciya.
Ayaba na dauke da sinadarin tryptophan, wanda jiki ke mayarwa zuwa serotonin wato wani sinadari ne da kwakwalwa ke taimakawa wajen sarrafa jin dadi da kwanciyar hankali.
Wannan na nuni da cewa cin ayaba na iya taimakawa wajen rage damuwa da gajiya ta kwakwalwa.
6.Sauran amfanin da dan Adam ke bukata.
Baya ga wadannan, Ayaba na dauke da sinadarin bitamin B6 wanda ke da matukar muhimmanci wajen samar da kuzari,da bunkasa lafiyar kwakwalwa da karfafa garkuwar jiki.
Haka kuma tana dauke da wasu bitamin da ma’adanai masu amfani ga lafiyar jiki.
Cin ayaba da safe wata hanya ce mai sauki kuma mai araha da za ta iya kara lafiya da kuzari ga duk mai son samun kyakkyawar Lafiya musamman tun daga safiya har zuwa dare kamar yadda masana suka tabbatar.

