Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, tare da kwamitin gudanarwarta, na bayyana alhini da jimami bisa rasuwar wasu mahajjata biyu da suka yi niyyar zuwa aikin Hajji, waɗanda suka rasu a wani mummunan hatsarin mota.
Mamatan sun haɗa da Alƙasim Ibrahim Walawa mai shekaru 48 da mahaifiyarsa, Hajiya Hadiza Garba mai shekaru 73.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar Rimin Gado zuwa cikin birnin Kano.
Marigayin Alƙasim ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya bakwai, yayin da Hajiya Hadiza Garba ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar.
Dukkansu ‘yan asalin ƙauyen Walawa ne da ke ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano.
Rasuwar tasu na da matuƙar taɓa zuciya, musamman ganin cewa suna kan tafiya mai albarka da nufin zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajji.
A cikin saƙon ta’aziyya,mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Alhazan Kano Alhaji Suleiman A Dederi hukumar da ma’aikatanta sun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya kuma karɓe su a Aljannatul Firdaus.
Haka kuma, sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah Ya ba su haƙuri da juriya a wannan lokaci na jimami.

