Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Najeriya ba ƙasa ce matalauciya ba, sai dai tana fuskantar matsalolin rashin daidaiton rabon arziki da ƙalubalen tsarin tattalin arziki.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan tattalin arziki, Tope Fasua, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a daina mayar da hankali kan taken “talauci”, a maimakon haka a mai da hankali kan hanyoyin magance matsalolin da ke haddasa shi.
A cewarsa, akwai alamun cewa tattalin arzikin ƙasar nan yana da ƙarfi, inda ya bayyana cewa bankuna sun tara sama da naira tiriliyan 4 a kwanan nan domin ƙara jari, kuma yawancin kuɗin sun fito ne daga cikin ƙasar.
Haka kuma ya ce kamfanin MTN na samun kusan kashi 40 cikin 100 na ribarsa daga Najeriya, abin da ke nuna akwai motsin tattalin arziki a cikin ƙasar.
Tope Fasua ya kuma ce babban ƙalubale shi ne rashin daidaiton rabon arziki, inda ya bayyana cewa akwai bambanci tsakanin masu kuɗi da marasa shi.
Ya ƙara da cewa kusan kashi 70 cikin 100 na tattalin arzikin Najeriya na aiki ne a ɓangaren da ba na hukuma ba , yana mai cewa sabbin gyare-gyaren haraji na gwamnati na nufin shigar da wannan ɓangaren cikin tsarin tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, ya bayyana kasafin kuɗin shekarar 2026 a matsayin mai cike da buri, yana mai cewa an ƙara fifiko kan ɓangaren ayyukan raya ƙasa.
Ya kuma ce bashin ƙasar ba ya wuce kima, yana mai cewa ana iya tafiyar da shi cikin tsari, tare da nuna kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya.

