Wata kungiya mai suna Haɗin Kan Jam’iyyar APC ‘Yan Dangole ta Jihar Kano, ta bayyana goyon bayanta ga yar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje wato Dr. Asiya Abdullahi Umar Ganduje da akafi sani da Balaraba a matsayin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kano domin raba gardama.
Jaridar Kano News 24 ta rawaito cewa Kungiyar ta bayyana cewa Dr. Asiya Ganduje mace ce mai kishin al’umma wadda ta dade tana hidimtawa jama’a, musamman matasa, ta hanyar shirye-shirye da dama da ke bunkasa rayuwarsu.
A cewar kungiyar, ta nuna kwarewa da jajircewa a fagen siyasa, tare da bayar da gudunmawa wajen samar da damarmaki ga matasa da mata a fannoni daban-daban da suka hada da ilimi, sana’o’i da dogaro da kai.
Haka kuma, kungiyar ta jaddada cewa Dr. Asiya Ganduje na da tausayi da hangen nesa wajen inganta rayuwar al’umma, tare da karfafa wa mata gwiwa su shiga harkokin siyasa da tattalin arziki.
Kungiyar ta kuma yabawa halayyarta ta hada kai da biyayya ga manufofin jam’iyya, tana mai cewa hakan ya sanya ta zama abin koyi ga mata da matasa.
Daga karshe, kungiyar ta bayyana cewa zaben ta a matsayin Mataimakiyar Gwamna zai taimaka wajen kawo ci gaba, hadin kai da wadata ga al’ummar Jihar Kano.

