Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta bayyana jin daɗinta da kuma yaba wa ziyarar da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa ya kawo jihar, tana mai cewa ziyarar ta zo a kan lokaci kuma ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai a tsakanin mambobinta.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar a jihar, Kwamared Auwalu Abdullahi Soja, ya fitar, ya ce ziyarar ta haifar da sabon ƙwarin gwiwa ga mambobin jam’iyyar a faɗin Kano, tare da ƙara musu amincewa da shugabancin APC a matakin ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa ziyarar ba wai kawai ta ƙarfafa haɗin kai ba ce, har ma ta nuna ƙudurin shugabancin jam’iyyar na ƙasa wajen kula da dukkanin ɓangarori da mambobinta.
Haka kuma, jam’iyyar ta yaba da yadda Shugaban Jam’iyyar na ƙasa ya kai ziyara ga tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanata, Malam Ibrahim Shekarau, da kuma fitaccen ɗan siyasa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, inda ta ce hakan alama ce ta girmamawa da kuma yunƙurin haɗa kan manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Jam’iyyar APC ta Kano ta jaddada cewa irin waɗannan matakai na nuna aniyar gina ƙarfi da daidaito a cikin jam’iyyar, domin tunkarar ƙalubalen siyasa da ke gaba.
A ƙarshe, jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa ƙofarta a buɗe take ga duk masu sha’awar shiga cikinta, tare da alƙawarin ci gaba da aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin bunƙasa jam’iyyar da kuma inganta harkokin siyasa a jihar Kano.

