Wani masani kan harkokin tattalin arziki,da tsare tsare a Najeriya Mr. Ayodele Adio, ya bayyana cewa attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote na nuna matuƙar tausayi ga ’yan Najeriya, yana mai jaddada cewa bai kamata a ɗora masa alhakin tsadar man fetur da ake fama da ita a ƙasar ba.
Mista Adio ya bayyana hakan ne a wata hira ta kai tsaye da akayi da shi a Truth TV inda yace hauhawar farashin fetur na da alaƙa da wasu muhimman dalilai da suka haɗa da yanayin kasuwar mai ta duniya,da tsadar shigo da kayayyaki, da kuma sauye-sauyen manufofin gwamnati.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/dangote-ne-ya-rage-farashin-fetur-da-kaso-5-6-shi-ya-sa-farashi-ya-sauka-ba-saboda-janye-harajin-15-ba/
Sai kuma babban dalili wanda ya janyo cikas shine yakin gabas ta tsakkiya inda ya ce waɗannan abubuwa ne da ke da tasiri kai tsaye kan yadda ake ƙayyade farashin fetur a cikin gida.
A cewarsa, duk da irin rawar da Dangote ke takawa a ɓangaren mai da makamashi, musamman ta hanyar sabbin matatun mai da ya kafa, ba shi kaɗai ne ke da ikon sarrafa farashin fetur ba, domin tsarin kasuwa da manufofin gwamnati na taka muhimmiyar rawa wajen tantance farashin.
Masanin ya ƙara da cewa sauyin darajar naira da farashin danyen mai a kasuwannin duniya na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara jawo tsadar fetur, yana mai cewa wannan lamari ya wuce mutum ɗaya ko kamfani guda.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/rage-farashin-fetur-da-mukayi-shine-dalilin-sauke-farashin-a-najeriya-ba-janye-harajin-kaso-15-ba-matatar-dangote/
Ya kuma buƙaci jama’a da su yi fahimta tare da kauce wa ɗora alhakin gaba ɗaya kan Dangote, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar tsadar fetur a Najeriya.

