Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana ranar 13 ga Mayu, 2026 a matsayin ranar da za a fara jigilar rukunin farko na alhazan jihar zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Babban daraktan hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara ta aiki da ya kai majalisar dokokin Jihar Kano, bisa ga jadawalin jigilar alhazai da hukumar Alhazai ta Ƙasa ta fitar kamar yadda mai magana da yawun hukumar a Kano Sulaiman A Dederi ya sanar
Ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan muhimman shirye-shirye da suka haɗa da tantance takardu,da tsare-tsaren jigila, da wayar da kai, da gwajin lafiya da kuma sauran matakan da suka dace domin tabbatar da an gudanar da aikin cikin tsari da kwanciyar hankali.
Alhaji Matawalle ya jaddada cewa yin bayani ga majalisar dokoki musamman Kwamitin Hajji kafin fara jigilar alhazai al’ada ce mai karfafa guiwa da kuma tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye suna tafiya yadda aka tsara.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi amfani da gogewarsa a harkokin Hajji tare da bullo da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da cewa alhazan Kano sun gudanar da ibadarsu cikin sauƙi, tsaro da cikakken kulawa.
Da yake jawabi tun da farko, Mataimakin Kakakin majalisar dokokin Jihar Kano kuma mamba a Kwamitin Hajji, Hon. Muhammad Bello Butu-Butu, ya taya babban daraktan murnar nadin da aka yi masa, yana mai bayyana cewa nadin ya dace da ƙwarewarsa da jajircewarsa.
Ya kuma tabbatar da cewa Majalisar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar domin ganin an cimma burin gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.

