Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu samari da mata biyar da ake zargin sun daura aure ba tare da izinin iyaye ko bin ƙa’idojin shari’a ba, a yankin karamar hukumar Nasarawa da ke cikin birnin Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa wanda ake zargi da daurin auren shi ne Aminu mai shekaru 23, wanda aka ce ya auri Sadiya mai shekaru 22, tare da Umar mai shekaru 24 da ya kasance wakilin ango, da Abubakar mai shekaru 23 wanda ya kasance waliyyin amarya, sai kuma Usaina mai shekaru 21 da wasu yan mata da suka kasance shedar daurin auren.
Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren ne kan sadaki na naira dubu goma (10,000), ba tare da amincewar iyaye ko izinin mahukunta ba.
Mataimakin babban kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman da kai simame Dr.Mujaheedden Aminuddeñ Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun kama mutanen ne bayan samun rahoto daga mazauna yankin da suka nuna damuwa kan yadda matasan suka gudanar da daurin aure ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya saba wa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin da ke kula da lamurran aure a jihar, tana mai cewa za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wanda ya karya tsarin shari’a a fannin aure.
A halin yanzu, waɗanda aka kama suna hannun hukumar domin ci gaba da bincike kafin mika su ga hukuma mai ruwa da tsaki don daukar matakin doka.

