Jihar Kano ta zama kan gaba a sakamakon jarabawar kammala sakandare ta bana (SSCE Internal) wacce hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandire ta kasa (NECO) ta gudanar.
Wannan bajintar ta zo ne sakamakon manyan gyare-gyare da jari mai yawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zuba a fannin ilimi tun bayan hawansa mulki.
Shugaban hukumar NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya bayyana sakamakon a Minna, dake jihar Neja, inda ya ce daga cikin dalibai miliyan 1,358,339 da suka rubuta jarabawar watan Yuni/Juli dalibai 818,492 kashi 60.26 cikin ɗari sun samu ƙwafin biyar ciki har da Turanci da Lissafi.
Haka kuma dalibai 1,144,496 kashi 84.26 cikin ɗari sun samu ƙwafin biyar da suka haɗa da sauran darussa ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba.
A sakamakon, Kano ta samu dalibai mafi yawa a jarabawar 68,159 (kashi 5.020 cikin ɗari na gaba ɗaya) da suka yi nasarar samun ƙwafin biyar ciki har da Turanci da Lissafi, inda ta fi kowace jiha. Legas ta biyo da dalibai 67,007 (kashi 4.930 cikin ɗari), sai Oyo da dalibai 48,742.
An danganta wannan nasara da manufofi da shirye-shiryen ilimi na gwamnatin Kano karkashin Gwamna Yusuf acewar mai Magana da yawun gwamnan Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa
A kasafin kuɗaɗen 2024 da 2025, ilimi ne ya samu kaso mafi girma, abin da ya bai wa gwamnati damar aiwatar da sauye-sauye masu tasiri.
Cikin su har da:
Raba kayan makaranta da kayan sakawa kyauta ga ɗalibai domin ƙara halartar makaranta.
Gyara da sabunta ɗakunan karatu da samar da kayan zama don inganta yanayin karatu.
Daukar malamai tare da basu horaswa akai-akai.
Ƙara tallafi ga manyan makarantu da guraben karatu ga ‘yan Kano.
Shirye-shiryen karfafa ilimin ‘ya’yan mata da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Wadannan matakai sun sa jaridun Leadership da Blueprint da kuma ƙungiyar malaman makaranta ta NUT suka karrama Gwamna Yusuf da lambar yabo ta “Gwamnan Ilimi na Shekara.
Da yake mayar da martani, Gwamna Yusuf ya bayyana farin ciki kan nasarar, inda ya ce hakan hujja ce cewa manufofin gwamnatinsa na tafiya daidai.

