Hukumomi da masana aikin noma a ƙasar Indiya sun ce sakamakon ambaliyar da ta mamaye wasu tarin gonakin jama’a, akwai barazanar samun raguwar aƙalla kashi 25 na shinkafar da aka fi sani da Basmati wadda ake fita da ita zuwa ƙasashen duniya daga yankin Punjab.
Ambaliyar ta bana wadda aka bayyana ta a matsayin mafi muni a cikin shekaru 40 da suka gabata, ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 30 a ƙasar, bayan ta shafi mutane sama da dubu 350,000, tare da hallaka dabbobi da kuma lalata kadarori daban daban.
RFI ta rawaito cewa masanan sun ce wannan ambaliyar ta bana ta mamaye gonakin da suka kai hecta 150,000 a Punjab mai ɗauke da mutane miliyan 30, abinda ya haifar da gagarumar asara ga manoman da kuma iyalan su, wanda ba’a taba ganin irin sa ba tun daga shekarar 1988.
Babban ministan dake kula da yankin Bhagwant Mann ya bayyana cewar, gwamnati za ta taimakawa manoman da wani bangare na diyya sakamakon iftila’in, lokacin da ya ziyarci ƙauyen Gatti Rajo dake yankin Ferozepur.
Ministan ya ce diyyar da za’a bai wa manoman ba wai zai tsaya ne ga gonakin su kawai ba, har ma da kadarorin da suka yi asara.
Manoman sun ce a wannan watan da ake saran girbe shinkafar da ambaliyar ta lalata, abinda ya daɗa jefa fargaba a kan farashin amfanin gonar a wannan lokaci.
Ramindra Singh Patiala, shugaban ƙungiyar manoman Punjab, ya ce ambaliyar ta mamaye ƙauyuka sama da 100 dake yankin Punjab.
Ƙungiyar masu safarar shinkafa zuwa kasashen ketare daga India, ta ce sakamakon wannan ibtila’i, za’a samu raguwar tsakanin kashi 20 – 25 na shinkafar basmati, la’akari da cewar jihar Punjab ce ke samar da kashi 40 da ake nomawa a cikin India, ko kuma sama da tan miliyan 6 kowacce shekara.

