Wani ɗalibi mai karatu a matakin shekara ta uku a jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Umar Abdullahi Hafizi, ya rasa ransa bayan da wasu da ake zargi masu kwacen waya ne suka kai masa hari suka daba masa wuƙa a gidansu dake Unguwar Dorayi,a ƙaramar hukumar Gwale da ke jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Lahadin data gabata a cikin gidan da mamacin ke zaune.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun kai masa hari,ne Inda suka daba masa wuƙa, sannan suka tsere da wayar salulansa.
Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar Bayero Malam Lamara Garba, ya bayyana mutuwar ɗalibin a matsayin babban rashi da kuma abin takaici ga al’ummar jami’ar, yana mai cewa duk da cewa harin ya faru ne a wajen harabar jami’a, suna aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin ganin an kama masu hannu a lamarin.
“Umar ɗalibi ne na sashen zaman takewa da Ilimin sanin laifuka wato Sociology and Criminology, mai halin kirki kuma haziki,Inji Sanarwar.
Jami’ar BUK na bakin cikin wannan rashi, kuma muna jajantawa iyalansa da abokan karatunsa,” in ji Lamara.
A halin yanzu, ’yan sanda sun cafke mutane huɗu da ake zargi da hannu a kisan, tare da kama wasu makamai kamar wuƙa da almakashi da ake zargin an yi amfani da su a kisan
Tuni aka kai gawar marigayin zuwa Zaria, Jihar Kaduna, wajen danginsa inda aka yi jana’izarsa bisa ƙa’idojin Musulunci.
Jami’ar BUK ta kuma ja hankalin ɗalibanta da su riƙa kula da lafiyarsu da tsaron kansu, musamman idan suna zaune a wajen harabar makarantar.
Ta kuma nemi jama’a da su taimaka da bayanai da za su iya sa a kama sauran masu hannu a wannan danyen aiki.
A ƙarshe, jami’ar ta Bayero ta bukaci ɗalibanta da su ƙara kula da tsaron kansu, tare da yin kira ga al’umma da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen kamawa da hukunta sauran masu hannu a lamarin.

