Rukunin kamfanin Dangote a bikin baje kolin kasuwanci na Kano na shekarar 2024 da ke gudana ya zama tamkar birnin Makka inda ya jawo kwararowar abokan huldarsa masu sha’awar yin tambaya da sayayya a yayinda kasuwar ke cigaba ta wakana.
Taron baje kolin wanda kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano (KACCIMA) ta shirya, mai taken “Ba a fitar da mai domin bunkasar tattalin arziki”, ya yi daidai da ra’ayin rukunin kamfanin Dangote na habaka tattalin arziki.
Sanarwa da Sashen Sadarwa na Rukunin Dangote ya sanyawa hannu ,yace bikin baje kolin kasuwanci da ya fara gudana daga ranar 23 ga watan Nuwamba zuwa 7 ga Disamba, 2024, ya sa rumfar Dangote ta himmatu wajen jan hankalin maziyartan tare da kebantattun teburan taimako don magance tambayoyi kan abinda ya shafi kamfanin
Ya kara da cewa: “Najeriya kasa ce mai samar da wutar lantarki da ba a fitar da mai ba, amma sai idan ta yi amfani da albarkatunta da dama. A Dangote mun nuna hakan ne da dimbin jarin da muka zuba a fannin takin zamani, sukari, gishiri da siminti da aka bazu a kasashen Afirka da dama.
Don haka kamfanin ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da damar wajen ziyartar rumfar kamfanin tare da cin gajiyar kayayyakin da aka baje kolin da suka hada da: Simintin , Dangote da Sikari da Gishiri da kuma Taki.
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya yaba da rawar da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya musamman Dangote.
Add A Comment