Babban Daraktan yada Labarai na gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya mika kyautar kudi naira miliyan 1 da dubu dari biyu ga daliban makarantar Islamiya ta Madarasatul Tahafizul Qur’an dake garin Yanoko a karamar hukumar Tofa a yayinda suka yi bikin saukar karatun Qur’ani karo na 22.
Taron bikin saukar wanda ya samu halartar manyan baki, ciki harda Sunusi Bature Dawakin Tofa,daliban sun samu wannan kyautar kudi ne a kokarinsa na bunkasa ilimi da kuma tallafawa dalibai.
A cikin tallafin kuɗin na naira miliyan 1 da dubu dari biyu, makarantar Islamiyar ta garin Yanoko ta samu naira miliyan 1 sai Kuma Malaman makarantar kowanne ya samu naira dubu 20 yayinda kuma daliban da sukayi sauka suka samu naira dubu biyar kowannensu.
Wannan tallafin kuɗin da Sunusi Bature ya bayar na daga cikin shirinsa na tallafawa al’umar yankinsa bayan kokarinsa na ganin ya ciyar da ilimi gaba.
Bayan Sunusi Bature Dawakin Tofa da ya bada kyautar sama da naira biliyan 1,Shima dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa da Dawakin Tofa Tijjani Jobe ya bada naira dubu 150 sai Shugaban karamar hukumar Tofa Yakubu Adis ya bada naira dubu 50 da Hon Adamu Mainasara da Sakataren karamar hukumar Tofa da suka bada naira dubu 30.
Sunusi Bature Dawakin Tofa ya nemi daliban da sukayi sauka da suci gaba da neman ilimi kada su tsaya iya nan.
Shugabannin makarantar Islamiyar ta Madarasatul Tahafizul Qur’an sun nuna gamsuwarsu kan gudun mowar da Bature ya basu,Inda sukayi fatan samun nasara akan abinda ya sanya a gaba.