Daga Sani Dan Bala Gwarzo
Jami’ar koyon kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya a garin azaren jihar Bauchi taci alwashin samar da walwalar Dalibai dake jami’ar.
Jami’ar ta ce zata gina dakunan kwanan dalibai da sanya duk abinda ake bukata domin saukawa daliban da suke zuwa daga nesa .
Mataimakin Shugaban jami’ar Farfesa Muhammad Audu shine ya bayyana hakan a yayin tattaunarwa da manema labarai a Katagun.
Farfesa Audu wanda yake karin haske a yayinda wakilan Kungiyar yan jaridu masu binciken kwakwaf suka karramashi a ofishinsa saboda gudun mowar da yake bayarwa ,ya shaida cewa zaici gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen Bauchi domin inganta walwalar Dalibai a jami’ar.
Ya godewa manema labaran da suka karramashi tare da shaida cewa zaici gaba da aiki dasu.
Ya kuma tabbatar dacewa, jami’ar zata cigaba da samar da kayan koyo da koyarwa domin inganta ilimin yara.
Ya kuma godewa dukannin ma’aikatansa da suke bada gudun mowa wajen cigaban jami’ar