Daga Musa Gama
Dalibi Bukhari Sunusi Idris daga jihar Kano ya zama zakara a gasar karatun kur’ani ta kasa karo na 39.
Musabukar ta Alqu’rani wacce cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto ta shirya an gudanar da ita ne jihar Kebbi .
Kwamitin amintattu na malamai karkashin jagoranci Farfesa Sa’adiya Omar OON da Mal. M.K. Jabo Mataimakin Shugaba, da sauran manyan malamai sune suka jagoranci tafiyar da musabukar.
Bukhari Sunusi ya fito ne daga karamar hukumar Gezawa .
Ya kuma lashe gasar karatun Qur’anin Hizifi 60 da tafsiri .
Sakamakon musabukar ya kasance cewa Bukhari Sunusi daga Kano wanda ya zamo na daya ya samu maki 98.20 cikin 100.
Sai Nuhu Muhammad daga Gombe da ya zama na biyu da maki 96.20 cikin 100.
Sai Mustapha Muhammad da ya zama na uku daga Kebbi da maki 95.30 cikin 100.
Sai Kuma Nafiu Ridwan Katsinawa daga Bauchi da ya zama na hudu da maki 93 .40 cikin 100.
Yayinda Kuma Safiyanu Muhammad daga Kaduna da ya zama na biyar da maki 93.10 cikin 100.
A wani karimci, Gidauniyar Ganduje foundation ta bayar da gudummawar Naira miliyan 2.25 ga wadanda suka yi nasara.
Gasar wacce aka gudanar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Jihar Kebbi, masu shirya gasar sun yaba da yadda aka kammala cikin nasara.
A wajen gasar an baiwa Bukhari Sunusi kyautar mota da kudade masu yawa.
Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III da gwamnan Kebbi Nasiru Idiris da Ministan kasafin kudin Abubakar Bagudu da manayan yan siyasa suna daga cikin mahalarta taron rufe musabukar.
Anan gaba ake sa ran gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai karbi bakuncin gwarzon shekarar dan karramashi