Rahotanni daga sassan jihohin Najeriya nacewa da yawa daga cikin gidanjen man fetur na NNPCL sun dauki tsawon mako daya a rufe duk da sanarwar rage litar man da akayi.
A ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2025 kamfanin NNPCL ya umarci wasu daga cikin gidajen man fetur a sassan Najeriya da su rage farashin litar man nan take.
Injiniya Nuraddeen Aliyu Wanda shine babban jami’in dake kula da gidan man fetur na NNPC dake tashar Kano line a birnin Kano kuma daya daga cikin Dillalan man daga kamfanin NNPCL shine ya shaidawa Jaridar TST Hausa tun a wancan lokacin,yana mai cewa a Jigawa an basu umarnin su sayar lita daya kan naira 975 a Kano kuma a sayar naira 965.
Saidai a wata ganawa karo na biyu da TST Hausa ta sake yi dashi,Injiniya Nuraddeen Aliyu yace rufe gidajen man fetur na NNPC da ake gani ,ya samo asali ne saboda wata sabuwar dabarar kasuwancin zamani da aka billo da ita.
Injiniya Aliyu yace a yanzu haka akwai wani Sabon tsari da kamfanin NNPCL ya fito dashi na sabunta yadda za’a rika dakon man fetur da sayar dashi a Najeriya,ta hanyar amfani da Na’ura ta zamani wanda shiyasa aka daina bada man fetur a gidajen na NNPC har sai an gama wannan sabon shiri.
Saidai babban jami’in yace kusan komai ya kammala, watakila daga yanzu zuwa kowanne lokaci mako za’a koma sayar da Man fetur a gidajen man na NNPC yadda ya kamata.
Ya kara dacewa ,ko a rumbunan ajiye man fetur akwai man a jiye ,Amma suna jiran umarnin daga sama domin fara raba man fetur din ,bayan kammala aiki akan wannan sabon tsari na tafiya da zamani wajen sayar da man fetur da dillacinsa a sassan Najeriya.
Rahotanni nacewa da yawa daga cikin gidanjen man fetur na Yan kasuwa suna sayar da lita daya tsakanin naira 1025 zuwa 1035.