Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulkin kasa inda ya zargi jam’iyyar da kaucewa akidar kafa ta,a yanzu ta buge da neman lalata Demokaradiyya.
El-rufai ya kuma zargi APC da maida hankali wajen shuka gurbataccen Shugabanci a Najeriya musamman a lokacin Tinubu.
Tsohon gwamnan, yayi wannan jawabin ne a wani taron manema labarai na kasa da ya gudana a Abuja kan karfafa mulkin dimokuradiyya a Najeriya.
El-Rufai, wanda ya wallafa matsayarsa a shafin sa na X ranar Talata, ya ce babbar damuwarsa a yanzu shine rashin tsarin tafiyar da dimokuradiyya a zamanin mulkin Bola Tinubu wanda ya zargi Tinubun da rusa tsarin siyasar APC da mulkin kama karya.
“Ni yanzu bana daukar APC jam’iyya,a Najeriya babu wata jam’iyya da ta samu nasara a cikin shekaru biyu sama da APC ,Amma mutum daya ya lalata ta”Inji tsohon gwamnan.
El-rufai ya yi Allah-wadai da rashin iya shugabanci daga APC.
Tsohon gwamnan ya bukaci jam’iyyun siyasa da su samar da ma’auni ga ‘yan takara da wakilai, yana mai jaddada cewa bai kamata kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada dama ga yan takara su rika gabatar da takardar shaidar kammala sakandare a matsayin mafi kankantar shaidar takarda da yan takarar zasu rika mikawa hukumar zabe ba.
Ya koka da cewa an yi watsi da manufofin da APC ta kafa na yaki da cin hanci da rashawa,da gina tattalin arziki, da inganta tsaro wanda yace akan haka aka kafa jam’iyar a shekarar 2013.
El-Rufai yayi hasashen cewa ba lalle ne kaso 75 cikin 100 na Yan Najeriya masu kada kuri’a su fito zaben shekarar 2027 saboda rashin iya shugabanci na APCn