Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yace lokaci yayi da zai fara yaki da masu hana Kano zama lafiya a duk Inda suke .
A yayin kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita tara, Gwamna jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya zare takobi wanda hakan ke nufi ya shirya tsaf domin yakar mutanan da ya kira azzalumai makiya jihar Kano da suka hana mutane zama lafiya.
Gwamna wanda ya karbi kyautar kwafin Al’qur’ani bugun hannu da kuma falleliyar takobi daga hannu Dr. Ishaq Falalu Zarewa a madadin al’ummar yankin bisa kammala aikin titin da ya tashi daga Fulatan zuwa Zarewa da kuma wanda ya taso daga Danguzuri zuwa Zarewa ,ya ce daga yau ya daura damara wajen yaki da cin hanci da rashawa,da zalunci da Kuma cutar da al’ummar jahar Kano ta kowanne bangare.
“Mun samar da wadannan tituna ne saboda bunkasa hada hadar kasuwanci da habaka harkar noma da kiwo domin cigaban wannan yanki” a cewar Gwamnan Kano
Wannan dai shine karu na uku da Gwamnan ya fito fili ya nuna shirin sa na yakar masu shirin tada fitina da rikici a jahar ta Kano Kamar Yadda Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanar.
Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaida aniyar gwamnan na ganin kano ta zauna Lafiya kuma ta kubuta daga hannun yan kama karya.