Jami’ar Northwest a Kano ta sallami dalibai 41 saboda samunsu da laifin magudin Jarabawa.
Jami’ar ta kuma hora dalibai 18 suma saboda samunsu da laifin hada kai wajen satar Jarabaawar.
Jami’ar ta dauki wannan matakin ne a zangon farko na shekarar karatu ta 2023/2024.
Jami’ar ta Northwest ta dauki wannan matakin ne bayan kammala zaman majalisarta karo na 56.
Shugaban sashen kula da jarabawar da daukar dalibai na jami’ar Northwest Jafaru Sule Muhammad shine ya sanar da daukar matakin cikin wata takarda da ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta yi nuni da cewa an samu daliban da aka kora da kuma wadanda aka hora saboda samunsu da aifin karya ka’idojin jarrabawar jami’ar.
Daliban da aka kora sun fito ne daga tsangayun jami’ar da suka hada kimiyar likitanci da sashen koyon Na’ura mai kwakwalwa da tsangayar Ilimi da tsangayar koyon tsarin gudanar da mulki.