Bayan shafe wata tara da rasuwar dan majalisar jiha mai wakiltar kananan hukumomin Bagwai da Shanono a jihar Kano Hon. Halilu Ibrahim Kundila al’ummar mazabarsa na zuba idanu domin ganin an maye gurbinsa ,dan cigaban yakin marigayin.
Mutanan kananan hukumomin biyu sun nuna damuwa game da yadda hukumar zabe ta kasa INEC ta gaza wajen shirya zaben maye gurbin dan majalisar tun bayan rasuwarsa.
Kundin tsarin mulkin Najeriya yayi tanadin cewa dole ne hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar da zaben cike gibi ga duk wani dan majalisa da ya mutu ko ya sauka cikin kwanaki 90.
Yanzu kimanin kwana 270 kenan ,babu wakilci a majalisar dokokin jihar Kano daga Shanono da Bagwai.
A ranar 7 ga watan Afirilun shekarar 2024 ,dan majalisar na jam’iyar APC ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Yanzu dai mazauna Shanono da Bagwai na ci gaba da dakon wakilci ,sannan kuma damuwarsu na karuwa a kowace rana.
A yayin ganawarsa da jaridar Daily Post,mai magana da yawun Shugaban karamar hukumar Shanono ,Ammar Wakili Shanono ya nuna damuwa kan wannan jinkirin daga hukumar zabe ta kasa.
Ya ci gaba da cewa, “Rashin wakilci da kuma gazawar INEC wajen gudanar da zaben cike gibin ya haifar da koma baya ga rayuwar al’ummar yankunan kai tsaye.
Ya ce ba a sanya wasu bukatu na al’ummar kananan hukumomin biyu a cikin kasafin kudin Kano na 2025 ba ,saboda rashin wakilci a majalisar dokokin Kano.
Ya yi kira ga hukumar zabe ta INEC da ta gaggauta ceto al’ummar yankin ta hanyar gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada.
Rahotanni nacewa illolin rashin shirya zaben sun bayyana a fili da suka hada da barin ayyukan samar da ababen more rayuwa da aka yi watsi da su,da matsalolin da ba a warware su ba a fannin ilimi da kiwon lafiya, da karuwar rashin aikin yi ga matasa.
Duk kokarin ji daga hukumar zabe ta kasa reshen Kano yaci tura
Amma wani babban jami’in hukumar zabe ta kasa reshen Kano da ya nemi a boye sunansa yace hukumar ta kammala dukkanin shiri kuma ana sa ran gudanar da zaben a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2025 ,bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan lamarin a mako mai zuwa.