Bayan kammala zaben shugaban kasa a kasar Amurka da Ghana, wasu kungiyoyin siyasa da masana siyasa sun fara hasashen cewa abinda ya faru a kasashen biyu na kayar da jami’ya mai mulki zai iya faruwa a Najeriya, a zaben 2027 .
Yan siyasar dake neman kada Shugaban kasa Bola Tinubu a Najeriya sun hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labor Party da Sanata Rabiu Musa kwankwaso na NNPP .
A kasar Amurka, tsohon shugaban kasar Donald Trump na jam’iyyar Republican shine ya doke Kamala Harris, mataimakiyar shugaban kasa kuma yar takarar jam’iyyar Democrat mai mulki a kasar a zaben da aka gudanar ranar 5 ga watan Nuwamban shekarar 2024.
Haka zalika, mataimakin shugaban Ghana Mahamudu Bawumia, dan takarar shugaban kasa na NPP mai mulki a kasar ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta NDC John Mahama, a ranar 7 ga Disamba, 2024.
Bayan zaben Trump,na Amurika da Mahama na Ghana jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara bayyana fatan cewa za su iya kwatankwacin samun nasara akan jami’yar APC mai mulkin a Najeriya a shekarar 2027.
Rahotanni nacewa sakamakon zaben Ghana shine ya sake sanya kwarin guiwa ga jam’iyyun adawa a Najeriya, yayinda suke kara kaimi na ganin cewa mulki ya bar hannun APC ,koda yake APC ma ita kadai tasan irin shirin da ta keyi.
A ranar 26 ga Nuwamba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-rufai sunyi wata ganawa dan samar da jami’ya guda daya da zasuyi amfani da ita a zaben 2027 duk dacewa basu fitar da wannan sanarwa a hukumance ba.
Bayan rahoton, Obi da Atiku sun sake haduwa a birnin Yolan jihar Adamawa, a ranar 30 ga Nuwamba, amma bangarorin biyu sun musanta cewa sun tattauna kan hadin gwiwa kafin zaben 2027.
Sai dai daga baya mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa shugabannin siyasar biyu sun yi ta tattaunawa a baya domin kada APC.
Haka kuma, a wata Asabar cikin watan , tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, a Abeokuta, jihar Ogun abinda ya dauki hankalin yan siyasa musamman jami’yar APC.
A cewar Kwankwaso, tattaunawar ta ta’allaka ne kan “muhimman batutuwan kasa da suka hada da makomar siyasa da shugabanci a Najeriya.
Yayin da haɓakar waɗannan ƙungiyoyin siyasa ke haifar da fata, yana kuma gabatar da ƙalubale masu mahimmanci ga yan siyasa a Najeriya.
A tarihin siyasar Najeriya sau daya ne kawai jam’iyyar adawa ta doke jam’iyya mai mulki.
A 2015, Buhari na APC ya doke Jonathan na PDP.
Buhari ya tsaya takara kuma ya sha kaye a zabukan shugaban kasa guda uku kafin jam’iyyarsa ta APC da ACN da kuma wani bangare na PDP (new PDP) suka hade a shekarar 2013 .
Hadakar dai ta samar da wani babban dandali domin cimma burinsa na shugaban kasa a 2015 da kuma sake tsayawa takara a 2019 wanda Buhari ya sake yin nasara.
Wanda ya dauki nauyin rubuta labarin.
Co-founder of Google and Brain, Andrew Nig computer Scientist