Majalisar wakilai ta Najeriya ta rarrashi Kungiyar Kwadago ta kasa NLC da ta janye aniyarta na fara zanga-zangar gama gari a sassan kasar nan domin duba masalahar yan kasa.
Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sadarwa shine ya rarrashi Kungiyar a madadin majalisar Inda kwamatin yace ya na tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya domin dakile zanga-zangar da za a yi a fadin kasar nan a ranar 4 ga watan Fabrairun 2025, saboda Karin kuɗin kiran waya da akayi da kashi 50 cikin 100.
A kwanakin baya ne hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da karin kuɗin kiran waya da Data da kaso 50 cikin 100 daga kamfanonin sadarwa, bisa la’akari da yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da ayyukansu.
Akan wannan yasa NLC ta shirya zanga-zangar gama gari a Najeriya a ranar Talata mai zuwa domin nuna fushinta akan karin kuɗin.
NLC tace zanga-zangar zata zamo a matsayin gargadi,saboda kokarin sake jefa yan Najeriya cikin wani hali na daban.
Kungiyar ta NLC tace a yayinda miliyoyin yan Najeriya har yazu basu warke daga tsadar rayuwa da aka jefa su sakamakon cire tallafin man fetur da Kuma tashin goron zabi na kayan masarufi ba ,ake nema a sake kawo maganar karin kuɗin kiran waya.
Da yake wata hira ta musamman da Jaridar PUNCH kan batun, Shugaban Kwamitin Sadarwa na Majalisar,wakilai Peter Akpatason, ya ce tuni kwamitin ya tuntubi NLC domin ganin ta dakile shirinta na fara zanga-zangar domin samar da zaman lafiya a Najeriya.
Akpatason wanda ke wakiltar mazabar Akoko-Edo a majalisar wakilai daga jihar Edo, ya bayyana cewa zanga-zangar da aka shirya idan aka bari akayita to za ta kara kawo wa ‘yan Najeriya wahala ne kawai.
Hakazalika, Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Reuben Mouka, ya shaida cewa suna iya kokarinsu domin fahimtar da NLC halin da ake ciki game da karin da akayi