Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi a gidansa dake jihar Adamawa.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka rabawa manema labarai wanda ya wallafa a shafinsa na X a yammacin ranar Asabar din nan.
Atiku wanda yace na karbi babban bako kuma abokina wato Peter Obi, a cikin ‘kasa mai kyau wato Adamawa
Bidiyon ya nuna shugabannin biyu, bayan sun gaisa kuma sunci abinci tare .
Duk da ba’a bayyana abinda suka tattauna ba amma na hasashen ganawar na da nasaba da zaben 2027
Wannan dai ba shi ne ganawarsu ta farko ba bayan zaben 2023,Koda a watan Mayun da ya wuce sun gana tare .
Haka zalika Obi ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki a gidansu dake Abuja a watan Mayu.
Ziyarar Obi ta kasance ganawarsa ta farko da tsoffin abokan siyasarsa bayan ya fice daga PDP zuwa labour party a watan Mayun 2022.
Mai magana da yawun kwamatin yakin neman zaben Peter Obi, Yunusa Tanko, ya ce tattaunawar da suka yi da jiga-jigan jam’iyyar PDP ta mayar da hankali ne kan yadda za a ceto Najeriya a 2027.