Daga Isha Muhammad Tambuwal
Yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan harin da sojojin sama suka Kai a Sokoto da ake cewa sojojin kuskure sukayi
Wasu hare-haren da sojojin Najeriya na sama da na ƙasa suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 10 da raunata wasu da dama.
Saidai rundunar sojojin tace an Kai harin ne saboda mutanan da aka kashe suna da alaka da lakurawa.
Babban jami’an yada labarai na operation fansar yamma Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi shine ya shaida hakan,Inda yace saida suka samu bayanan sirri kafin sukai harin ,a dan haka yace ba kuskure ba ne.
Amma gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu da yakai ziyarar jaje garuruwa biyu da aka jefa Bama Ban ya kira harin da cewa yana kama da kuskure idan akayi la’akari da cewa daga cikin wadanda suka mutu ,harda kanana yara da mata.
Yace zasu gudanar da bincike dan gano hakikankin dalilan sakin bama baman akan wadanda basuji ba basu gani ba.
Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da jami’an sojin suka kai hari kan ƙauyukan, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar da abun ya faru Abubakar Muhammad ya tabbatar .
Shugaban ƙaramar hukumar, Abubakar wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana’izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce “jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai” a kan ƙauyukan.
Ya ƙara da cewa “Sojojin sama ne da na ƙasa suka kai harin, sojojin sama sun shiga yankin da manyan tankokin yaƙi.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce baya ga mutum 10 da suka mutu, akwai kuma mutum shida da suka samu raunuka.
Ƙauyukan na kusa da jejin Surame da ake ganin maɓuyar mayaƙan ƙungiyar Lakurawa da ta ɓulla a ƙasar a baya-bayan nan.
A lokuta da dama sojojin Najeriya kan yi kuskuren kai hare-hare kan fararen hula, lamarin da a wasu lokutan ke haddasa mummunan asarar rayuka.
Ko a watan Disamban 2023 ma, wani jirgin sojin Najeriya maras matuƙi ya kai hari kan masu Mauludi a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, lamarin da ya haifar da asarar rayukan mutane sama da 95, da jikkata wasu da dama.