Daga Muslim Muhammad Yusuf
Tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, ya ce ‘yan Arewa ba su da hujjar kalubalantar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ko kin sake zabansa a shekarar 2027.
Shehu Sani, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP kuma mai rajin kare hakkin bil’adama, ya ce ’yan Arewa masu adawa da kudirin gyaran haraji na Tinubu tun a baya sune suka kasa kalubalantar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fara jefa Arewa cikin kangin talauci.
Shugaba Tinubu ya mikawa Majalisar dattawa kudirin sake fasalin haraji a shekarar da ta gabata amma kudurin ya janyo ce-ce-ku-ce daga masu ruwa da tsaki a yankin Arewa.
Daga cikin masu sukar Dokar harda gwamnoni,da dattawan Arewa da sarakunan gargajiya,da kungiyoyin farar hula .
Sai dai Shehu Sani, a wata hira da ya yi da manema labarai, a Abuja ya bukaci yan Arewa da su sake shirya kansu domin ganin yadda ’yan Arewa da ke cikin gwamnatin Tinubu za su ba da gudummawar ci gaban yankin tun kafin lokaci ya kure musu.
Ya ce Buhari ya nada ‘yan Arewa mukamai da dama a gwamnatinsa amma ba su iya taimakon yankinsu ba, ya kara da cewa ‘yan Arewa a zamanin Buhari sunki bari fadawa masa gaskiya ko sukae salon mulkinsa,duk da yawan kura kuran da yakeyi ,sai Yanzu da sukaga yadda Tinubu ke kokarin mayar da Arewa saniyar ware , mutanan da suka fito daga yankin Arewan suke son yin magana bayan Kuma lokaci ya kure musu ,acewar Shehu Sani.
Yace da yawa daga cikin yan arewan ne Kuma suka sayar da yancin mutanansu a zaben 2023 da ya gabata ta hanyar tallata Bola Tinubu.
Shehu Sani yace Yan Arewa basu da bakin magana a yanzu,tunda basu iya yin magana a zamanin Buhari ba.
Ya nuna damuwarsa kan yadda yan Arewa suka suka sayar da yancinsu a wajen Tinubu kafin zaben 2023.