Gwamnatin Kano ta yi karin bayani kan rabon awaki 7,150 da aka rabawa mata 2,000 a jihar Kano a ,wani mataki na shirin bunkasa kiwon dabbobi da tallafa wa mata domin dogaro dakansu.
Shugaban hukumar kididdiga ta jihar Kano, Dr, Aliyu Isa Aliyu, ya ce rabon ya biyo bayan rahoton kididdigar kasa na 2024 da ya nuna cewa jihar Kano na da kaso mai tsoka a bangaren iya kiwon dabbobi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dr Aliyu ya bayyana cewa wannan tsari zai karfafa tattalin arziki tare da bunkasa rayuwar mata a jihar Kano.
Ya nuna mamakinsa kan yadda bangaren adawa ke sukar wannan shiri, alhalin kuma a bayyane take cewa kiwo na da asali a cikin addinin islama,sannan kuma abu ne dake kawo riba cikin hanzari.
Dr Aliyu Isa Aliyu ya kara da cewa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya wanda Kano ta fito daga nan yana samar da kaso 33% cikin 100 na jimillar kiwon dabbobin da kasar nan keyi , inda jihar Kano ke da kaso 8% na wannan adadin.
Ya kara da cewa jihar Kano ita ce kan gaba wajen yawan gidajen gona a Najeriya, wanda hakan ya sa shirin rabon awakan ke da muhimmanci ga jihar a irin wannan lokaci.
Dr. Aliyu ya kawo misalin da shirin kiwon macizai da kwadi da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki, ya kawo a jihar Jigawa a zamanin mulkinsa wanda ya bunkasa tattalin arzikin jihar
Yace indai ba’a soki salon kiwon macizai ba ,to babu dalilin da zaisa a soki kiwon awaki a Kano.
Ya yi kira ga al’ummar Kano su kalli shirin kiwon akuya da kyakyawar fahimta saboda tasirin da hakan zai yi ga tattalin arzikin jihar.
Aliyu ya karyata rade-radin cewa an kashe naira biliyan 2.3 kan sayen awakan Inda ya ce wannan kudin an ware su ne domin aiwatar da gaba dayan tsare-tsaren bunkasa kiwon awakan a jihar Kano kashi na daya zuwa na uku.
Ya ce shirin ya gudana ne a matakai uku Inda Kashi na farko aka raba awaki guda 7,150 ga mata 2,000 sai kashi na biyu Inda aka raba shanu 1,342 yayinda mataki na uku aka raba tumakai 1,822.
Ya ce duk wanda ke da korafi ya kamata ya kalli shirin a gaba dayansa, ba wai ya tsaya kan rabon akuya ba kawai.
Dr. Aliyu ya jaddada cewa gwamnatin Kano tana bin tsare-tsaren da suka dogara da ilimi da bincike domin aiwatar da duk wasu manufofinta.
Ya yi kira ga mutane da su daina kallon abinda gwamnati tayi ta fuska daya idan ya zamo dole sai sunyi adawa.