Ma’aikatan Najeriya sun sake neman Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kara musu albashi da a kalla 50 cikin 100 akan Karin da akayi musu na baya.
Ma’aikatan sunce saboda tsadar rayuwa ya zama wajibi Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya duba halin da ma’aikata suke ciki domin kara musu albashin.
Ma’aikatan sun nemi karin albashin ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar DAILY POST ta yi da wani babban jami’in kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, wanda ya bukaci a boye sunansa.
Bukatar karin albashi ya zo ne watanni shida bayan karin mafi karancin albashin ma’aikata a watan Yuli, 2024.
Ma’aikatan dai na son kwamatin kula da tattalin arzikin kasa da ya duba halin da ma’aikata da sauran yan Najeriya suke ciki domin kawo sauyi mai dorewa.
Babban jami’in Kungiyar ta NLC ya kara dacewa , manufofin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na yiwa tattalin arzikin kasa garambawul basa aiki.
Ya kara da cewa sunyi taro da sakataren gwamnatin tarayya da ministoci kusan bakwai ko takwas a kwana kwanan nan kuma akwai yiyuwar a sake duba taswirar karin albashin.
Bayan da manema labarai suka tuntubi mai magana da yawun kungiyar ta NLC, Benjamin Upah da sakataren ta na kasa Emmanuel Ugboaja, basu samu damar amsa wayar da akayi musu ba.
Idan dai za a iya tunawa, Tinubu, ya amince da karin mafi karancin albashi na naira 70,000, maimakon naira naira 250,000 da yace zai biya amma idan yan Kwadago suka yarda ya kara kudin man fetur,inda a wancan lokaci aka tsaya akan naira dubu 70 saboda yan Kwadagon sunki amincewa a kara kudin man fetur din.
Shugaban Kungiyar NLC na Najeriya Joe Ajaero,a wancan lokacin ya tabbatar da matsayin da suke kai na amincewa da naira 70,000 ga ma’aikata kuma akan haka ake biya a yanzu.
Duk da karin mafi karancin albashi da Tinubu ya amince da shi, a watan Yulin shekarar da ta gabata, hauhawar farashin kayan abinci da Kuma kare Karen kuɗaden man fetur ya janyo karin kuɗin albashin bai amfanar da ma’aikatan Najeriya yadda ya kamata ba.