Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu ta sanar da cewa a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2025 take son fara amfani da dokar haraji ta 2024.
Dokar harajin idan har majalisar dattawa ta amince da ita ,ta kunshi sauye-sauyen haraji guda hudu da zata fito dasu daga majalisar.
Shugaban kwamitin fadar Shugaban kasa kan samar da sauye sauyen dokar harajin Mista Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a Legas.
Kwamitin shi ne ke Jagorantar gyare gyare a cikin dokar harajin wacce tasha zazzafar suka daga bangarori daban daban musamman Arewa.
Saidai kurar ta fara lafawa ne bayan kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Alhamis ta goyi bayan dokar.
Majalisar dattijai kuwa a ranar Juma’a 17 ga watan Janairun shekarar 2025 ta bayyana gamsuwarta kan yadda gwamnonin suka amince da dokar harajin.
Shima Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa gwamnonin abisa hadin kan da suka nuna wajen amincewa da dokar tare da bukatar majalisar dattawa ta gaggauta amincewa da ita.
A ranar 28 ga watan Janairun 2025 majalisar dattawa za ta koma cigaba da zama bayan kammala hutun Kirsimati da sabuwar shekara.
Oyedele, wanda yake magana a wani taro na masu ruwa da tsaki a Lagos ,ya ce ana sa ran majalisar zata amince da wannan doka kafin watan Maris, yayin da za a ci gaba da shirye-shiryen fara aiwatar da ita cikin watan Yuli.
Yace Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana son fara amfani da dokar akan lokaci shiyasa ya tsayar da watan na Yuli.
DP