Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe korafe ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace shinkafar Tinubu da aka kama a Kano takai darajar Naira Biliyan 1 da kusan rabi.
Hukumar ta kama shinkafar ne ana sauya mata mazubi a wani waje dake titin ring road cikin karamar hukumar Nasarawa.
Barista Muhyi yace an kama shinkafar ne dauke da hoton shugaban kasa Bola Tinubu wacce aka kawo Kano dan tallafawa mutane a watan Azumin Ramadan dake shirin zuwa a bana .
A zantawarsa da manema labarai ,Barista Muhyi yace an karkatar da shinkafar ne kuma a kalla tirela 28 aka sauke na shinkafar aka boye .
Hukumar ta yaki da cin hanci ta Kano ta kama mutum daya da ake zargi kuma za’ci gaba da bincike dan gano sauran mutanan da ake zargi.