Sakataren gwamnatin jihar Ondo, Tayo Oluwatuyi, ya mutu a wani hadarin mota.
Sakataren gwamnatin ya mutu ne a hadarin da ya afku a lokacin da yake kan hanyarsa ta barin Akure, babban birnin jihar Ondo, zuwa Ibadan a jihar Oyo.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan yada labarai na jihar Ondo, Wale Akinlosotu, ya bayyana cewa saida aka kai Oluwatuyi Asibiti kafin ya mutu a Asabar din nan da rana.
Hadarin ya faru ne makonni biyu da suka wace.
Kwamishinan ya bayyana Sakataren gwamnatin jihar ta Ondo Oluwatuyi a matsayin ma’aikacin gwamnati mai kwazo wanda jajircewarsa na tafiyar da harkokin mulki, ya haifar da cigaba sosai.