Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya amince da murabus din sakataren gwamnatin jihar Barista Ibrahim Muhamamd Kashim.
A Wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar M. Gidado ya fitar, ta nuna cewa gwamna ya amince da murabus din na nan take.
A cewar sanarwar, gwamna Bala Muhammad ya umurci shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Dakta Aminu Hassan Gamawa da ya karbi ragamar aikin ofishin taohon Sakataren gwamnatin a matsayin mukaddashi.
Gwamna Bala ya godewa Barista Kashim bisa irin ayyukan da ya yi wa jihar a lokacin da yake rike da mukamin SSG.
TST Hausa ta rawaito cewa har yanzu tsohon Sakataren gwamnatin jihar bai bayyana dalilansa na sauka daga aiki ba.
TST Hausa ta kuma rawaito cewa gwamna Bala Muhammad ya nada Barista Ibrahim Kashim Sakataren gwamnatin jihar a ranar 15 ga watan Yuni na shekarar 2021 bayan ya rasa takarar gwamnan jihar a shekarar 2019 .
Sannan gwamna Muhammad na Bauchi ya sake nada Barista Kashim bayan a karo na biyu ya sake rasa takarar gwamna a zaben shekarar 2023