Baban Daraktan kula da ayyuka na musamman a fadar gwamnatin kano AVM Ibrahim Umar mai ritaya yace gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf zai kaddamar da Asusun tallafawa iyalan sojojin da suka rasa rayunsu a fagen daga.
Daraktan yace gwamna Yusuf zai kaddamar da asusun tallafawa iyalan yan zaman jiya ne a ranar litinin,a fadar gwamnatin kano,duka a wani bangare na bikin ranar tunawa da yan mazan jiyan.
AVM Umar mai ritaya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a ofishinsa kan shirye shiryen taron da za’ayi na bikin tunawa da sojojin kasar nan na shekarar 2025.
A cewarsa, gwamna Yusuf ya kuma shirya jagorantar bikin ajiye furanni,a makabartar yan mazan jiyan a garin Dotsa da ke karamar hukumar Kumbotso ranar Laraba domin girmama Sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yiwa kasa hidima kuma suka rasa rayukansu.
Bayan bikin girmama Sojojin, za a yi liyafar cin abincin rana a ofishin Kungiyar ta Kano.
Babban daraktan ya bayyana cewa, a duk ranar 15 ga watan Junairun kowace shekara ne ake bikin ranar tunawa da Yan mazan jiya.
Ana bikin ne domin karrama wadanda suka yi yakin duniya na daya da na biyu da kuma yakin basasar Najeriya.
AVM ya jaddada cewa wannan rana nada mahimmaci wajen bayar da agaji ga sojojin da suka samu raunuka daban-daban a yakin da ake yi da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas tare da magance wasu matsalolin tsaro na cikin gida dake addabar jama’a.
AVM Umar ya yaba da kyakykyawan hadin gwiwa tsakanin ofishinsa da bangaren yan jarida a fadar gwamnatin kano inda ya bada tabbacin ci gaba da aiki tare domin amfanin ‘yan jihar.