Daga Muslim Muhammad Yusuf
Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da yunkurin kashe Sanata Lawal Adamu Usman, mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, inda ta bayyana lamarin a matsayin babbar barazana ga dimokuradiyya.
A wata sanarwa da Engr. Sanusi Sarki, mai magana da yawun kungiyar magoya bayan PDP a yankin Arewa maso Yamma ya fitar, ya bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.
Kungiyar ta kuma bayyana harin a matsayin na “masu daukar siyasa a mutu ko a yi rai” tare da jaddada bukatar hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) su bankado tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kungiyar ta bayyana muhimmancin irin gudunmawar da Sanata Usman ya bayar ga al’ummar mazabar sa, wanda a tunaninsu hakan ne ya haifar da kishi daga wasu yan siyasar.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa irin wadannan hare-hare ba abu ne da ba za a amince da su ba a tsari na dimokuradiyya, inda ta bukaci ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a Kaduna da su gaggauta daukar matakin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Sarki ya kuma shawarci shugabannin siyasa da su kasance masu taka-tsan-tsan da jam’ian tsaro a koda yaushe.
Kungiyar magoya bayan PDP ta yi kira ga mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, da ya tabbatar an gudanar da bincike na cikin gida kan lamarin inda suka nuna damuwarsu kan abin da suka ce da gangan aka yi domin kawo barazana.