Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya rage farashin litar mai zuwa naira N899 kowace lita.
Kafin hakan ana sayar da litar man fetur din akan naira 1,020 zuwa 1,050.
Kungiyar dake kula da kadarorin albarkatun man fetur (PETROAN), ta ce kamfanin na NNPCPL ce ta kayyade sabon farashin.
Da yake kafa hujja da wata takarda da sashen kasuwanci na NNPCL ya fitar, jami’in hulda da jama’a na kungiyar ta PETROAN na kasa, Dokta Joseph Obele, ya ce an rage farashin ne daidai da nisan kowacce shiya a Najeriya daga bakin teku.
Rahotanni nacewa wannan cigaban yazo ne kwanaki biyu bayan da matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N899.50k ga ‘yan kasuwa albarkacin ranar kirsimati da sabuwar shekara
Add A Comment