Daga Salisu Isa Galadanci
Zauren hadin kan malamai da kungiyoyin addinin musulunci na Najeriya sun nuna gamsuwarsu kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na kwashe kananan yaran da suke gararamba akan titunan Kano ana killacesu .
Shugaban Kungiyar zauren Malaman reshen Kano Ferfasa Musa Muhammad Borodo shine ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci malamai domin kai ziyara wajen da ake tsare da yaran da aka kwashe tare da basu kulawa, daga bisani Kuma a sadasu da iyayensu.
TST Hausa ta rawaito cewa hukumar Hisba ta Kano ce ta kwashe duk yaran da suke gararamba akan titunan birnin Kano Inda ake kula da tarbiyarsu a sansanin hukumar Alhazai ta Kano.
A kalla yara kanana 250 hukumar Hisba ta kwashe a karo na farko.
Ferfasa Muhammad Borodo ya kara da cewa, akwai bukatar hadin kan al’umma da kuma sauran masu ruwa da tsaki dake fadin jihar nan domin ganin aikin kwashe kananan yaran ya samu nasara.
Da yake nasa jawabin sheikh Abdulwahab Abdullah yayi kira ga iyaye dasu ci gaba da kulawa da yayansu domin sauke nauyin da Ubangiji ya dora musu.
Ya kuma godewa gwamnatin Kano da kuma shugaban kwamatin kwashe yaran karkashin jagorancin sheik Aminu Ibrahim Daurawa abisa kulawar Mataimakinsa Dr Amenuddeen Mujahideen saboda namijin kokarin da sukayi wajen kwashe yaran.
Ko a farkon shekarar 2024 hukumar Hisba ta Kano ta mayar da yaran da aka turo Kano karatun Allo zuwa gaban iyayensu wadanda daga bisani suka kara dawowa birnin Kano
Shiek Abdulwahab ya nuna irin hadarin dake tattare da kwanan karkashin Gada da tashohin mota da kuma kasuwannin da almajiran ke zama.
Daga bisani zauren hadin kan malamai da kungiyoyi na jihar Kano, sun tabbatar da cewa, zasu bada dukkanin hadin kan da ake da bukata domin ganin shirin ya samu nasara kamar yadda aka tsara.