Yayin da ya rage kasa da mako guda a fara bikin Kirsimati, a sassan Duniya ciki harda Najeriya zurga-zurgar jiragen sama a Najeriyar musamman a yankin Kudu maso Gabas yayi tashin goron zabin da ba’a taba gani ba.
Rahotanni nacewa ana sayar da tikitin hawa jirgin sama tsakanin naira 680,000 zuwa naira 700,000 duk mutum daya.
A wani bincike da jaridar LEADERSHIP tayi da kuma lekawa zuwa shafukan yanar gizo na kamfanin Air Peace,da United Nigeria Airline,da Ibom Air,da Arik da Aero Contractor ya nuna cewa farashin tikitin shiga jihohin Kudu maso Gabas ya yi tsada matuka.
Wannan yanayi ya jefa fasinjojin dake son hawa jirgi cikin fargaba musamman masu kokarin kaucewa barazanar tsaro.
Jihohin da biranen da lamarin ya shafa sun hada da Anambra,da Enugu da Owerri, da kuma Fatakwal a yankin Kudancin Najeriya.
Amma kuma rahotan ya nuna cewa farashin tikitin jiragen sama a sauran jihohin Najeriya ba su kai na yankin kudu maso gabas ba.
Misali, tikitin hawa jirgin daga Legas zuwa Anambra yana kan naira 700,000, yayinda jirgin Abuja zuwa Owerri a kan naira 550,000.
Bugu da kari daga Legas zuwa Enugu a ranar 26 ga Disamba fasinjoji sun biya naira 400,000.
Rahotanni sun tabbtar dacewa an samu hauhawar farashin tikitin jirgin sama a yankin na kudu maso gabas,ne saboda yawan masu bukatar yin tafiye tafiye zuwa yankin ko fita daga yankin.