Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna gamsuwarsa kan yadda Kungiyar matan Yan sandan Najeriya (POWA) ke taimakon masu rauni daga cikinsu.
Daga nan yace zai baiwa Kungiyar ta POWA fili kyauta nan da watanni uku masu zuwa domin samar da babbar sakatariya a Kano.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne lokacin da yake karabar bakuncin Shugabar Kungiyar matan yan sandan Najeriya Mrs Dr. Elizabeth Kayode Egbetokun, a ofishinsa dake fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Yusuf yace Kungiyar tana iya kokarinta wajen bada magani a Asibiti da sauran bada tallafin kayan abinci da sauransu.
Daga nan ya yabawa kwamishinan yan sanda Kano CP Salman Dogo Garba abisa hadin kan da yake baiwa gwamnatinsa wajen samar da tsaro ga al’umar Kano.
Ya nemi matan yan sandan Najeriya da suci gaba da bada hadin kai ga mazajensu domin cigaban Najeriya musamman a bangaren tsaro.
Daga nan Shugabar Kungiyar matan yan sandan Najeriya Mrs Elizabeth Ebatekun ta karrama gwamna Yusuf abisa jajircewarsa wajen sauke nauyin al’uma.
Kafin Kungiyar ta bar kano,saida ta bude Sabon Asibitin data gina domin kula da matan yan sandan da sauran marayu da ake kula da su.