A kokarin da ake na kare rayukan kananan yara da aka haifa a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da ayyukan rigakafi na yau da kullum, wadanda aka yi watsi da su na tsawon watanni 18 a karkashin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Rahotanni nacewa daga farkon wa’adinsa a 2023, Gwamna Yusuf ya ba da fifiko ga lafiyar mata da yara, yana mai nuna matukar damuwa kan dakatar da shirye-shiryen rigakafi ga yara kanana da tsohuwar gwamnatin Ganduje tayi watsi dashi.
A wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnan kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, yace gwamnan ya ba da umarnin gaggauta dawo da wadannan muhimman ayyuka tare da ba da tabbacin samar da kudade ga aikin rigakafin a matakin jiha da tarayya.
A yayin kaddamar da kashi na biyu na makon lafiyar mata da jarirai na shekarar 2024, Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na rage mace-macen mata da kananan yara.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa kasafin kudin jihar Kano na shekarar 2024 ya hada da samar da kwakkwaran tanadi na ayyukan rigakafi,da tabbatar da dorewar shirin da kuma isa ga kowa Kano.
Sunusi Bature yace yunkurin da Gwamna Yusuf ya yi ya nuna aniyar gwamnatinsa na magance matsalolin kiwon lafiya da kuma inganta rayuwar mazauna Kano.