A cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano yace nadin ya fara aiki nan take .
Sauran mutanan da Gwamna Yusuf ya nada sun hada da Dr Ibrahim Musa a matsayin mai bashi shawarar kan harkokin kula da lafiyar alumma.
Sauran masu bashi shawarar sun hada da Dr. Hadiza Lawan Ahmad Mai bada shawara kan zuba jari da Barista Aminu Hussain mai bada shawara kan shari’a da harkokin kundin mulki da Ismail Lawan Suleiman mai bada shawara kan kidaya da Nasiru Isa Jarma Mai bada shawara kan harkokin kungiyoyi.
Gamnan ya kuma nada wasu shugabanin hukumomi a Kano
Sannan gwamna ya tayasu murna