Daga Musa kallamu Yola
Jam’iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki sun goyi bayan gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad a kan matakin da ya dauka na yin watsi da dokar gyaran haraji ta 2024 da yace an shirya ta ne domin kuntatawa talakawan Najeriya musamman yan Arewa.
Idan za’a iya tunawa a ranar Litinin 30 ga watan Disamba na shekarar 2024 ne fadar shugaban kasa ta bukaci gwamnan na Bauchi a cikin sa’oi 24 ya janye kalamansa akan dokar harajin da kuma furacin da yayi akan Shugaban kasa Inda fadar tace hakan kokari ne na tada hankalin al’ummar Najeriya.
Mai baiwa Shugaban kasa Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwar jama’a, Mista Sunday Dare, ya bayyana hakan a wani sakon da ya rabawa manema labarai a Abuja.
Gwamnan na Bauchi ya fito ya nuna adawa da manufofin Shugaba Bola Tinubu na sake fasalin harajin, inda ya kwatanta su a matsayin “masu adawa da arewa” da kuma fifita wani bangare na kasar nan kawai.
Lokacin da suke kare gwamnan na Bauchi Bala Muhammad, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, na Najeriya, Shugaban riko na PDP na kasa Umar Damagum, da sauran masu ruwa da tsaki a jami’ar sunce babu wani abu da zai furgita su .
Damagum, wanda ya bayyana kudirin a matsayin cin mutuncin jama’ar Najeriya, ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta kama hanyar ruguza Najeriya ta hanyar karbo basussukan kadade daga kasashen waje.
Da yake mayar da martani,Shima ga fadar ta Shugaban kasa Darakta Janar na kungiyar gwamnonin PDP, Emmanuel Agbo, ya jaddada cewa shugaban kungiyar gwamnonin PDP Kuma gwamnan Bauchi na da yancin fadawa Yan Najeriya halin da ake ciki Inda Shima yace babu wata barazana da zatayi aiki akansu.