Magoya bayan jam’iyyar NDC mai hamayya a birnin Accra sun fatsama kan tituna domin yin murnar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar.
Tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya taka rawar gani a siyasance, bayanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a yammacin Afirka, bayan da abokin hamayyarsa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye.
Tun kafin ranar zaben ,masana siyasa a kasar Ghana suke hasashen cewa abinda ya faru a Amurika na nawowar Trump shine zai faru a Ghana.
Mahama ya mulki Ghana tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017
Da yake jawabi ga manema labarai daga gidansa, Bawumia ya ce ya kira Mahama ya taya shi murna, ya kara da cewa jam’iyyar NDC ta Mahama ta lashe zaben ‘yan majalisar dokoki.
Ɗan takarar na jam’iyya mai mulki ya kuma ce jam’iyyar hamayya ta NDC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.
Har yanzu Hukumar zaben kasar Bata bayyana yawan kuri’un da kowa ya samu ba