Al’umar garin Gboko a jihar Benue sun samu kansu cikin farin ciki da walwala jim kadan bayanda kamfanin siminti na Dangote tare da wasu al’ummomi shida da suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da tarihi (CDA)
Yarjejeniyar da aka fi sani da Dangote Cement ga ayyukan raya miliyoyin nairori, an yi bikin ne a matsayin wani muhimmin ci gaba, tare da al’ummomin da suka yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna.
Mai Martaba, Ter Gboko, Gabriel Shosum,ya yaba da yarjejeniyar wanda yace zata taimaka wajen tabbatar da inganta tattalin arziki.
Sarkin ya kuma tabbatar dacewa al’ummomin da suka dade suna nema burinsu ya cika yanzu lokaci yayi.
Daga nan Sarkin ya mika godiyarsa ga shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote bisa jajircewarsa na magance bukatun al’ummomin yankuna da dama a Najeriya harma da kasashen waje.
Misis Bimbo Sariat Olawoye, wacce ta wakilci ministar ma’adinai ta kasa, ta bayyana farin cikinta da wannan nasara da aka samu tare da yin kira da a hada kai don ganin an aiwatar da cikakken shirin na yarjijeniyar
Anasa jawabin tunda farko shugaban karamar Hukumar Gboko Hon. Elias T. Yina, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wacce ba ta misaltuwa a cikin tarihin kamfanin sama da shekaru 40, inda ya bayyana yuwuwar sa na cin gajiyar ba wai kawai ga al’umar sa ba harma jihar Benue da kasa baki daya.