Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike yace shugaban kasa, Bola Tinubu ya kashe sama da naira biliyan 300 domin samar da tauraron dan Adam a kananan hukumomin Abuja a cikin watanni 17 da suka gabata.
Minista Wike yace an samar da tauraron dan Adam din ne domin bunkasa harkokin sadarwa ,da samar da bayanan sirri dan samar da tsaro a Abuja da kuma samar da cigaba a zamanance a bangaren kimiya da fasaha.
Ministan ya bayyana haka ne a yankin Ibwa da ke karamar hukumar Gwagwalada lokacin da ya kaddamar da fara amfani da sabon titin Paikon Kore zuwa Ibwa mai tsawon kilomita 9, wanda ya lashe kudi naira biliyan 8.5.
Yace yanzu haka Shugaban kasa Bola Tinubu na aikin gina titin Aguma Palace zuwa Titin Kasuwa wanda shima zai lashe kudi naira biliyan 22,yana mai cewa za a fara amfani da titin a watan Mayun bana.
“Mun kammala aikin gina makwrantu da dama kuma muna ci gaba da gyara wasu a yankin karamar hukumar ta Gwagwalada domin mu bunkasa Ilimi”Inji ministan.
Ministan yace idan akayi kiyasi kan jimillar kudaden da Shugaban kasa ya kashe wajen samar da ayyukan raya kasa ,a kasa da shekaru biyu a iya Gwagwalada kadai, sun haura naira biliyan 50.