Gwamnatin jihar Kano taci alwashin kawo karshen yawaitar tara shara akan titunan birnin Kano da wasu wurare da ake tara sharar ba bisa ka’ida ba.
Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano wacce zata jagoranci wannan shiri da hadin guiwar ma’aikatar sufuri da ta kasuwanci a jihar Kano, ana sa ran shirin zai taimaka domin magance matsalar tara shara akan titunan birnin Kano.
Kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dr.Dahiru Muhammad Hashim ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da shirin kawar da shara da sarrafata shirin da aka kaddamar a kasuwar Kantin Kwari ranar Litinin.
Kwamishinan yace a yanzu haka an dawo da yawancin ma’aikatan shara da aka daina gani a baya zuwa kan tituna da wuraren da ake tara shara a birnin Kano domin tabbatar da shirin.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da gangamin aikin , kwamishinan ya ce taron ya nuna jajircewar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na ganin jihar Kano ta kasance mafi tsafta, da koshin lafiya,da Kuma kyawun muhalli a Najeriya.
Kwamishinan Hon. Hashim ya ce dawo da masu aikin shara akan titunan birnin Kano zai taimaka wajen tsaftace birnin Kano da kewaye.
Daga nan yace ma’aikatar ta fara biyan kudaden alawus-alawus din ma’aikatan shara na gwamnatin jihar kan lokaci domin kara musu karfin guiwa.
An kaddamar da fara aikin kwashe sharar ne a kasuwar Kantin Kwari kan titin IBB,Kuma acewar kwamishinan daga litinin din nan za’a daina ganin tilin shara akan titunan Kano