Majalisar Dokoki ta jahar kano ta bukaci kungiyoyi masu zaman kansu a jahar da su rubuto bukatar samar da dokar da zata tsaftace sana’arsu musamman yadda ake kuka da matasan da suke sace kayan amfanin jama’a, suna sayarwa .
Mutanan gari sunsha yin korafi da Yan Jari Bola musamman wadanda basusa rijista suna cire kofofin godaje da tagogi ko wani abu mai amfani na gida .
Shugaban kwamitin majalisar me kula da kasafin kudi kuma wakilin karamar hukumar Ungogo Hon. Aminu Saad Ungogo ya bukaci hakan a lokacin taron sauraron ra’ayin Jama’a bayan da wasu kungiyoyi Suka bayyana koken su game da yadda masu sana’ar gwangwan suke barazana ga kaddarorin Jama’a.
Aminu Sa’ad Ungogo yace majalisar Dokoki tana sauraron kungiyoyin su kawo kudirin dokar a rubuce domin daukan matakin daya dace akan su.
Wannan matsalar ta dade tana damun Jama’a, don haka kuzo da kudirin doka ga majalisar Dokokin, mu kuma zamu ga yadda zamu yi da su” inji Dan Majalisar
Wakilin karamar hukumar Ungogo a majalisar dokoki ta kano yace masu fakewa da sana’ar sun dade suna barna ga kaddarorin gwamnati, inda yace akasarin makarantun gwamnati da sauran kaddarorin da gwamnati ta samar, wadanda aka yi su tun tale tale da , irin wadannan matasa sun balle karafan sun sace, wanda yace idan ba a dauki mataki ba, to lamarin zai kai inda ba a zato.
“Irin wadannan mutane dake fakewa da sana’a, duna barnata kayan gwamnati da aka Samar da su tun kafinna a haife mu, da wadan da aka Samar da su a lokacin mu don son zuciya, wadan da in ba a dau kataki kan yadda za a tsaftace harkar ba, to lamarin zai cigaba” a cewar Hon. Aminu Saad Ungogo.
Sai dai kuma, wasu kungiyoyin a lokacin taron, sun bada shawara kan a karfafa baiwa yara ilmi da sama wa matasa abin dogaro da Kai, wanda hakan zai rage samun matasa dake fakewa da sana’ar su yiwa kayan Jama’a illa.